“Karen da ya sha kwai a kansa takan kare”
jeudi 9 mars 2006 par Arimi Abba
Yau idan aka dubi irin tabarkazar da ake ci gaba da tafkawa a ma’aikatun gwamnati, abin sai du’a’i, kama tun daga fannin shara’a, ilimi, kiyon lafiya, tsaro da dai sauran makamantansu, gaba daya sun fi karfin talaka ya ci moriyarsu kai tsaye ba tare da cin hanci ba. A kan haka ne ma kungiyar nan ta duniya mai suna (Transparancy International) mai gwagwarmayar kare hakkin dan Adam, ta jera kasar Nijar a sahun kasashen da su ka yi kaurin suna ta fannin cin hanci da karbar rashawa, wanda hakan ba karamin abin kumya bane ga kasa da kuma al’ummarta baki daya. Duk da cewa mun sani tun fil’azal kasar Nijar na fuskantar irin wannan matsala ta cin hanci da rashawa, wato tun lokacin mulkin soja, amma hakan bai hana mata shakat ba, sai wajejan shekarar 1987 lokacin mulkin janar Ali Saibu, wanda lokacinsa ne mahukumtan wannan lokaci su ka yi rabon gado da dukiyar kasa da tsohon shugaba Janar Saini Kunche ya mutu ya bari. Kadawar guguwar mulkin Demokradiya ta 1990 kawo yau shekaru 16 ke nan, kasar Nijar ta tsinci kanta a cikin mummunan halin Allah kama hannu na, inda cin hanci da rashawa su ka zama rowan dare a cikin ma’aikatu. Kama tun daga kan minista har zuwa masinja, sun zama yan rashawa. A bangaren shara’a kuma, abin ya fi bada tsoro inda kirikiri ana ji ana gani ake danne mai gaskiya a gasgata makaryaci, wannan kuwa ya samo asali ne ganin cewa an fitar da shara’a daga hannun malamanta, yanzu ta koma ga hannun mahukumta, su kama wanda su ke so su kuma saki wanda su ke so. Hakan kuma ya kara yawaita karbar hanci da rashawa tare da handamar dukiyar gwamnati ga yan gaban shara’a wadanda ganin sun fi karfin shara’a. saboda su na takamar cewa su na da kariyar shuwagabannin siyasa, ganin haka su ma na kasa da su su ka dogara da wane ya yi ba’a hukumtashi ba ni ma mi zai hana in yi. To wannan shi ne halin da kasar Nijar ta tsinci kanta a ciki. A saboda haka yanzu za’a dora wa alhakin faruwar haka ga kasar Nijar? Amsa ita ce shugaban kasa, domin shi ne jama’ar kasa ta zaba, kuma shi keda hurumin tsaida shara’a ta gaskiya da adalci ga al’umma, kamar yadda idan kasa ta yi kyau shi za’a ce. A dalilin haka a cikin jawabin barka da sabuwar shekara ta 2006 da babbar alkalin kotun koli ta kasar Nijar Madam Bazai ta yi wa shugaban kasa Tanja Mamadu, ta fada masa gaskiya tare da dora alhakin faruwa duk wata tabargaza da ta shafi cin hanci da rashawa tare da tabarbarewar shara’a a wannan kasa, inda ta nunuar da cewa lokaci ya yi da ya kamata shugaban kasar ya zage damtse, domin magance wannan babbar annoba da ta mamaye kasar ta na neman halakata. Ta fuskar shara’a kuma Madam Bazai ta ciji yatsa kwarai da aniya, inda ta ce al’amarin ya lalace, shara’a ta fita daga matsayinta da aka santa da shi ta mai zaman kanta, ta koma hannun yan siyasa, sun mayar da ita wani dandali na biyan bukatun kansu. Dan haka Madam Bazai ta yi fatan ganin ba tare da bata lokaci ba shugaban kasa Tanja ya dauki matakan maido shara’a a cikin hayyacinta ma’ana ga malamanta, in kuwa ba haka ba, nan gaba ba a san cikin mawuyacin halin da kasar za ta ida fadawa ba. A lokacin da ya ke karbar barka da sabuwar shekarar da ga makaraban gwamnatinsa, Frayiminsta Hama Amadu ya fito karara ya nuna irin yadda cin hanci da rashawa ya yi kaka gida a cikin ma’aikatun gwamnati, inda ya ce ma su ya na sane da duk irin tabargazar da ake tabkawa, dan haka ya ja hankalinsu da su dauki matakai magance matsalar a cikin wannan sabuwar shekar ta 2006. Sai dai kuma anya wadannan surutai sun isa su kawo karshen wannan matsala kuwa? ni dai a ganina a’a, hanya guda ce wace ta fi saukin magance lamarin shi ne a faro bincike tun daga sama ayo kasa, ma’ana tun daga zauren shugaban kasa da shugaban gwamnati in dai da gaske ake ana bukatar shawo kan matsalar kenan a ba gawa kashi dan mai rai ya ji tsoro. Tunatarwa sanin kowane dan kasa ne shugaban kasa da Frayiminstansa kadai su ka sha Alkur’ani mai tsarki, a kan cewa za su tabbatar da gaskiya da adalci a cikin wannan kasa ta Nijar, dan haka su san fa da cewa “Karen da ya sha kwai to fa a kansa takan kare” sai asan mafita.
Mahaman Salisu Hamisu
Site réalisé avec SPIP 1.9.2c + ALTERNATIVES
