Ni suna na Rabilu Musa Dan Lasan, wanda aka fi sani da Dan Ibro .An haife ni ne a garin Dan Lasan na karamar hukumar mulkin Warawa dake jahar Kano tarayyar Najeriya, shekaru na ba su wuce 31 ba, a yanzu ina zaune a garin Wudil dake cikin jahar Kano, ina da mata guda biyu da yaya na 8. >suite
A ranar asabar 22 ga watan janairun da ya gabata ne gidan Radion Tambara tare da hadin guiwar wasu matasa yan kasa da ke nan birnin Yamai, suka gayyato yan wasan kungiyoyin dake shirya fina-finan hausa na tarayar Najeriya suka gabatar da wata gagarumar wasa da ta kayatar da yan kallonta a babban dakin wasannin motsa jiki na Palais des sports dake nan birnin yamai, da kuma a gidan kallon Cinéma Zabarkan. Daga cikin yan wasan da aka gayyato sun hada ne da Ali Nuhu, Sani Danja, Aina Ade, da dai sauransu...wannan ya baiwa jaridar Ra’ayi damar tattaunawa da shahararren jarumin nan kuma Director mai shirya fina-finan hausa da tauraruwarsa ke cigaba da haskawa ta wannan fage, wato Ali Nuhu. Da farko dai jaridar Ra’ayi ta soma tambayar sa ne da cewa : >suite
A fagen wasannin motsa jiki, kasar Nijar tayi fice matuka dangane da nuna kwarewa ta fannin kokowar gargajiya, inda a koda yaushe a kace za’a gudanar da wata kwambala, to lalle yan Nijar a shirye suke domin kare martabar kasar su. >suite