Alternative Espaces Citoyens Niger

Fira da Musa Cangari Babban Magatakardan Kungiyar Alternative Espace Citoyen (AEC) Yamai

lundi 8 novembre 2010 par Souley Magé Regeto

Shugaban kasar Cana Hu Jintao ya kai wata ziyar aikin kwana uku a kasar Faransa, daga ranar 4 zuwa 7 ga watan Nobamba na shekarar 2010. A karkashin wannan ziyar aiki, shugaban kasar Cana Hu Jintao da takwaransa na kasar Faransa Nikolas Sarkozi sun rattaba hannu a kan wasu yarjejeniyoyi na kwagila tsakanin kasashen biyu, wadanda suka ba Faransa damar samu tsabar kudin Amirka dala miliyan dubu 20 daidai da kudin Faransa (Yuro) miliyan dubu 14 ke nan. A cikin kwangilolin suka shiga tsakanin kasashen biyu, akwai wadda ta shafi karfen Yuranium wanda kampanin Areva na kasar Faransa ke haka a cikin karkarar Arlit yakin Agadez Jamhuriyar Nijar. Kasar Cana da kasar Faransa, kasashe biyu ne dake huldar tattalen arziki da kasar Nijar musamman a kan abin da ya shafi ma’adannan kasa. To ko wadannan yarjejeniyoyi na iya taba tattalen arzikin kasar Nijar ? Me kuma yan kasar Nijar ke fargaba a ciki ? Ga nazarin da Malam Musa Cangari Babban Magatardan Kungiyar Alternative Espace Citoyen (AEC).

Malam Musa Cangari ya fara da cewa : tabbat duk abubuwan da suka wakana, sun shafi kasashen biyu, kuma sun shafi kasar Nijar. Dalilin da yasa suka shafi Nijar, shi ne, a cikin yarjejeniyoyin da suka sa hannu, akwai wadda ta shafi hakar karfen Yuranium, wanda kampanin AREVA na kasar Faransa ke haka a jamhuriyar Nijar yau fiye da shekaru 40. sanin kowa ne, a da kampanin Areva kadai ne ke hakar wannan karfe a doron kasar Nijar. To amma a cikin yan shekarun nan shuwagabanin kasar Nijar sun bude kasuwar samun kwangilar hakar Yuranium ga kowa, wato kowace kasa ta duniya na iya ta zo a yi yarjejeniya da ita saboda ita ma ta nemi wani abu daga cikin arzikin ma’adannan kasar da Allah ya albarkanci Nijar da su. A cikin kasashen da suka samu wannan kwatara ta hakar Yuranium, akwai kasar Cana wadda ta samu har da ta tonon man petur. Sanin kowane lokacin da wannan yarjejeniya ta shiga tsakanin kasar Nijar da Cana kampanin Areva bai ji dadi ba. Wato banda wurare biyu da kampanin Areva yake da shi, wato na SOMAIR da COMINAK, Areva ta so ta samu wani lasisin buda wani sabon kampanin hakar Yuranium, wannan kuma shi ne na IMURAREN. Shi ma da kyar da walahau la suka same shi, saboda kasar Nijar ta nemi a kara kudin Yuranium. Bayan ja-in-ja tsakanin kasar Nijar da Areva aka samu yarjejeniya wadda ta ba su damar tonon rijiyar ta IMURAREN. A yau ita ma kasar Cana tana nan, ke nan Areva ta samu kishiya, wato ana iya a ce Cana ta shigo gonar Areva. Shigowar Cana da wasu kasashe cikin gonar ta Areva ya ba yan kasar Nijar damar cewa, tun da masoyan Nijar masu yawa ne, irin su Kanada da Indiya da Ostaraliya da dai sauransu, ko ina mana da masoya, wato masu bukatar su ma su shigo su hako wannan karfe na Yuranium da wasu ma’adannan kasa, ke nan wata dama ce gare mu da za mu sayar da kayanmu ga wanda muke so kuma da daraja. Wannan bai yi ma Areva dadi ba. To ita ma karsar Cana ta yi yarjejeniya da kasar Nijar.

A yarjejeniyar da ta shiga tsakanin Cana da Faransa, ita Areva ta bada shawarar kasashen biyu su hada gwiwa. Su hada gwiwa tsakaninsu su biyu, don saboda harakar nukileya gabadaya. Wato tun daga hako karfen Yuranium har zuwa sarrafa shi zuwa ga wani makamashi ko wani makami mai lizzami, duk dai abin da ake iya yi da Yuranium. Takamaimai dai shi ne suna son su yi aikin tare da Cana. Tuni dai a cikin yarjejeniyar sun yi dahir da cewa, kampanin Areva za ya ba kasar Cana ton dubu 20 na karfen Yuranium kowace shekara, har tsawon shekaru 10 a nan gaba. Banda wannan kuma, za su kafa wani kafani na sarafa nukileya tsakaninsu. Haka kuma suka yarda a kan za su aikin tare da kasar Cana a kamfanin hakar karfen Yuranium na Imuraren, wato kasar Cana zata daukar wani hannun jari a cikin kamfanin na Imuraren. Idan suka cimma haka, ke nan kasar Cana da Faransa bakinsu daya, babu gasa tsakaninsu. Idan kuma tabbat ta kasance haka, kasar Nijar ba zata ji dadi ba. Saboda idan babu gasa tsakaninsu, wato idan ba su kasance kishiyoyin juna ba, to abin ba ya gyra kasar Nijar. Amma in akwai gasa tsakaninsu, to a duk lokacin da kasar Nijar ta gano da ba ta jin dadi aiki da wani daga cikinsu, sai ta je wajen wacan ta ce masa kai me ka ce? Wato abin kamar ka je kasuwa ne, idan ya kasance dan kasuwa daya ne ke sayar da wani abu, to yadda ya gadama zai sayar. To amma idan yana da abokan gasa, to sai ka kewaya wajen wanda za ku jituwa. Yau Nijar, ita ce ke da karfen Yuranium na saidawa, ke nan in akwai masu bukata da dama, irinsu Cana da Indiya da Ostaraliya da Faransa da Kanada da dai sauransu, sai ta tsayar da kudin karfen Yuranium yadda ta gadama, mai bukata ya saya, wanda kuma bay a iyawa sai ya bar wuri. Hakan kuma zai sa kasashen su yi kokowa domin kowa ya samu shiga. Amma in har ya zamanto bakinsu daya, to kamar mutum daya ne ke gaban kasar Nijar, bata iya buga teburi ta ce ga yadda take so a yi. Wannan yarjejeniya da ta shiga tsakanin Cana da Faransa ta nuna cewa, ba wai masu gasar juna ba ne. Lokacin da shugaban kasar Nijar ya nemi a kara darajar farashen karfen Yuranium, da bay a kasance akwai wasu kampanonin kasashen duniya dake bukatar ba, wadanda suka bayyana, da Areva da kasar Faransa ba za su yarda a kara wani abu ba ga yadda ake a da. To amma da yake akwai su, Areva da Faransa sun yarda, saboda sanin cewa, kasar Nijar na iya ce masu, ba su kadai ke bukatar ba, za a bada kwangilar ga wasu mabukata. Yanzu kuma sun kewaye kasar Nijar, sun je, sun hada baki da kasar da take takama da ita, wato Cana, ke nan yanzu tamkar kasa daya ce ke hakar karfen na Yuranium. A cikin yarjejeniyar da suka yi, akwai wadda ta hada kampanin nukileya na kasar Faransa da Cana, haka kuma akwai ta wani kampanin hakar man petur na kasar Faransa da na Cana. A nan ma kasar Nijar na iya fargaban cewa, watakila, a nan gaba suna iya suyi wani hadin gwiwa a kan hako man petur ma. Sanin kowane, kasar Cana ce ta samu lasisin hakar man petur din kasar Nijar, har ma da na matatar man petur din. Ke nan suna iya cewa, yadda muka bude maku shiga hakar Yuranium ta Imuraren, kuma ku bude mana hakar man petur. Ta nan suna iya samun gamin baki. Wannan kuma ya kamata ya ja hankalin yan kasa, saboda kasar Nijar ce ke da Yuranium da man petur dinta, amma wasu kasashen ketare can ke wani hadin gwiwa a kan hakarsu. Rishin tsoma kasar Nijar cikin wannan yarjejeniya, Wato kafata ba tare da shawartar Nijar ba, nada alaka da yadda muka yi yarjejeniya da kasashen masu hakar ma’adannan kasa. Da ya kasance a cikin yarjejeniyar mun ce, kamar kowane kampani zai alaka ko kafa wata yarjejeniya da wata kasa, sai an yi shawara da kasar Nijar za a yi haka, wato ya shafeta, to da a nan kasar Nijar zata iya fitowa ta ce ma kasar Faransa, kampanin SOMAIR da COMINAK da na IMURAREN da muka ba ku, ba don ku hada da wasu ba ne. Da kasar Nijar ta ce sai a yi shawara da ita da haka ne. A lokcin da ake zazzafar rigima a kan farashen Yuranium, akwai wani kampani na kasar Kanada, wanda shi ma ya samu lasisin izinin hakar Yuranium din. Shi ma wannan lasisi, Areva ce ta kewaya ta saye shi daga hannun kasar ta Kanada. Wato lasisin da kasar Nijar ta hana mata, ta bayar da shi ga kasar Kanada ya zama nata. Hada baki tsakanin Cana da Faransa, daga baya suna iya saye duk wani lasisi da aka ba wata kasa ko wani kampani, wato komai ya zama a hannunsu. Wato ya zama aikin mutum daya. Ba kuma abin mamaki ba ne Areva ta saye duk wani lasisi na kasar Cana. Ana iya zaton watakila abin ba zai yiyuwa ba, amma kuma ba za a fitar da tsammani ba. Bayan haka, wannan hadin kai tsakanin Faransa da Cana yakan iya taba farshen da aka tsayar tsakanin kasar Nijar da wadanda ta ba lasisin hakar ma’adannan kasar. Saboda da ma ba da son Areva aka basu lasisin ba, ya zama cilas ne. In ma ba su sauke farashen ba, suna iya hana ma kasar Nijar fitowa da wata hujjar nuna wata bukatar kara farashen. Dalili kuwa shi ne, sun yi baki daya, to ga wa Nijar zata dogara ta ce masa, shi tana son ya gyara zamansa da ita. Wannan kuma tabbat wani cikas ne. Bisanin wannan hadin gwiwa suna iya cewa, a je a yi magana da kasar Nijar ta rage farashe.

Abin lura a nan shi ne me? Kasar Faransa tana jan kokari ne don ta rike matsayinta da darajarta a yankin Sahel gabadaya, musamman ma a kasar Nijar. Wato ta rike makaminta na sahun gaba kuma ita ce kasar da ake aiki da ita. Yanzu ma idan aka dubi harakar ga ta Alka’ida wadda ke gudana a cikin arewacin kasar Nijar, kasar Faransa ta zo da sojojinta a cikin kasar Nijar, wannan kuma wani abu ne da ba a taba gani ba. A da sun zauna da wani karamin sansanin soje a kasar Nijar, amma yau da shekaru da dama da suka bar wuri. Yanzu, kuma watakila suna da niyar kafa ta su barikin soje a kasa. Wato kamar yadda suka yi a kasar Cote D’Ivoir da sauran kasashen Afrika. Sun nemi su kai sojojinsu a kasar Mali amma abin ya ci tur, amma sun je su yi wata yarjejeniya da kasar Moritaniya, wadda zata kawo sojojinta a kasar Mali, don su yi kokowa da alka’ida. Amma kuma ai manazarta da dama sun gano da cewa, bayan kasar Moritaniya, Faransa ce ke labe tana jagorancin dukan abubuwa. Su kuma kawo wasu yan sojoji a kasar Burkina Faso.

A shekarun baya Amirka ce ta kawo wani shiri na yaki da ta’addanci, ta kawo sojojinta da manema labarai da dai sauransu dake aiki da jami’an tsaron kasa. Wani tsari ne da suka so daukar duk yankin na Sahel ta hanyar wani furoje mai sunan PAN SAHEL INITIATIVE. Amirkawa ne ke wannan aiki tare da sojojin kasar Nijar da na Mali da dai sauransu. Yanzu ita ko Faransa na son ta shigo wannan aiki, saboda tana ganin kamar Amirka ta shigo gonarta ne. wato yanzu Faransa ta dawo da karfi tana son ta kula da duk wannan yanki na kasashen da ta mallaka. Dalili kuwa shi ne arzikin ma’adannan kasa da yankin ya kunsa, ke nan ba za su yarda ba wadansu su dauka ko su tona. Dole ita Faransa ta kare matsayinta na wadda ta mallakin kasashen a da. Wannan kuma wani sabon salo ne na mulkin mallaka suke kokarin asassawa. Abin da ya yi masu sauran yanzu shi ne, su samu damar kafa sansanin sojojinsu, watakila ma su shiga cikin harakokin zaben shuwagabaninmu. Saboda hakan zai ba su damar samu wani Karen farautarsu, dan amsar Shatansu, wanda zai kare duk wani alfanu nasu a cikin yankin. A taikaice dai wannan yarjejeniya ta shafi kasar Nijar gadan-gadan, amma da yake ba mu da bakin Magana, ana iya a zalumce mu ta wannan hanya.


Accueil du site | Contact | Plan du site | Espace privé | Statistiques | visites : 632990

Suivre la vie du site ha  Suivre la vie du site Hausa  Suivre la vie du site Labarun Nijar   ?

Site réalisé avec SPIP 1.9.2c + ALTERNATIVES

Creative Commons License